• Home
  • Media
  • Languages
  • Free Stuff
  • Contact Us

Lessons in:
  • English
  • Français
  • Hausa
  • Yoruba

PostHeaderIcon KAI KIRISTA NE?

PostAuthorIconWritten by Henry M. Bikang | Print | E-mail

"Sa'anda ya same shi,ya  zo da shi Antakiya. Suna nan fa a tattare chikin ekklesiya har shekara guda fa chika,suna koya ma mutane dayawa; a chikin Antakiya fa aka fara che da masu-bi Kirista". Ayukan Manzanni 11:26.

Ta yaya mutum zai zama mai bi kuma a che da shi Kirista?.

Zama mai bi ko Kirista ba ta wurin iyayen kaba. Kuma ba ta wurin bayasuwa ba, ba ta wurin arziki ka ba. Kuma ba wurin yawa yin adua'a ba. Kuma ba ta wurin karanta Littafi Mai-Tsarki ba. Ba kuma ta yawan zuwa majami'a ba.

TA YA YA KUMA ZAKA ZAMA KIRISTA KO MAI BI?.

Matta 28:19 Ku tafi fa, ku almajiratadda dukan al'ummai, kuna yi masu baptisma zuwa chikin sunan Uba da na Da da na Ruhu Mai-tsarki".

Wannan umurni Yesu Kristi ne ga me da hanya da mutum zai zama mai bi.

Bari mu duba yadda mutane  sun zama Kirista a chikin Littafi mai-Tsarki.

1.YAHUDAWA A RANA FENTECOST.

Wato mutum dubu uku suka yi baptisma a wannan rana. Ayukan Manzanni 2:36-42. A nan wandannan su zama masu bi ta wurin ji maganar Allah. Su tuba baya haka sai an yi musu baptisma domin gafarar zunubai su. A wannan rana a yi masu baptisma.

2.MUTUMIN HABASHA.

Wannan mutumin baba mai sarauta dayawa kal-kashin kandakatu,sarauniyar Habashawa. Wannan mutum ya zama mai bi ta wurin ji maganar Allah, kuma ta wurin bada gaskiya, sai a yi masa baptisma. Wannan Habashi ya je Urushalima domin yi sujada ga Allah amma a karshe ya ba da gaskiya har an yi masa baptisma a rana  nan a chikin ruwa domin ya zama mai bi. Domin ya samu ceto,domin ya zama kirista. Ayukan Manzanni 8:26-38.

3.KIRISBUS SHUGABAN MAJAMI'A DA IYALIN SA DA MUTANE KORINTIYAWA.

A nan mun ganni Kirisbus shugaban majami'a da iyalinsa da mutane korintiyawa su ba da gaskiya sai an yi masu baptisma domin su zama masu bi na nufi Allah. Domin su zama Kirista kamar yadda Litafi Mai-tsarki ta fadan. Su yi wannan baptisma domin su samu ceto 1 Bitrus 3:21,Markus 16:16; domin a wanke zunubai su Ayukan Manzanni 22:16.

Bari mu duba Ayukan Manzanni 18:8 ta che wa "Kirisbus kuma, shugaban majami'a, ya bada gaskiya ga Ubangiji tare da gidansa duka; mutane dayawa kuma daga chikin korinthiyawa aka yi masu baptisma"

Inda  ka na so zama mai bi na gaskiya dole sai ta wurin ji maganar Allah da ku bada gaskiya ga Yesu sai a yi maka baptisma.

Kai ma ka yi tunani kamar yadda  Kirisbus shugaban majami'a ya yi.

4.LIDIYA DA IYALIN TA.

Wato mata nan mai suna Lidiya i ta mai sujada ga Ubangiji ne. Amma da ta ji wa'azi wanda zai sa ta mai bi, ko kuma Kirista, tayi na'am da managanar  Allah yar an yi ma ta baptisma da iyalin ta wandan su kai baptisma Markus 16:16. Karanta Ayukan Manzanni 16:13-15. Sun yi baptisma domin su zama masu bi.

5.YARI KURKUKU A FILIBBIYAWA.

Wannan mutum ya zama mai bi a ta wurin ji maganar Allah a ta baki Bulus. Mutumin nan ya yi taibaya cewa "Ku shugabanai , sai in yi minene domin in tsira?". Sai Bulus ya amsa masa da yi ma shi wa'azi maganar Yesu Kristi.

A chikin tsakiyar dare Bulus da Sila suka yi ma wannan mutum baptisma da iyalinsa da su kai a yi ma su baptisma. Karanta Ayukan Manzanni 16:25-34. Sun zama masu bi chikin dare domin ba  su

se randa zai su mutum ba.

A BIN LURA:

Da shi ke mutum ba se ran da zai mutu ba ko kuma rana dawo Yesu Kristi, sai ya yi baptisma aran da ya ji wa'azi bishara Yesu.

Haka littafi mai tsarki da mu duba ya ce babu bata lokacin da yi baptisma.

- Zama mai bi fa ,sai ta wurin wannan baptisma a chikin ruwa. Ayukan Manzanni 10:47 8:36-38.

- Zama mai bi fa sai a yaife ka ta wurin ruwa da Ruhu Yohanna 3:3,5.

- Zama mai bi fa sai a bizne ka a chikin Kristi, ta wurin mutuwa sa kuma ka tashi tare da Yesu ta wurin baptisma Romawa 6:3-4.

- Zama mai bi fa sai an gafarta maka zunubai ta wurin yi baptisma Ayukan Manzanni 2:38.

- Zama mai bi fa sai ka sani cewa a kwa baptisma daya Afisawa 4:4.Shi ne  mu totone a wanna koyarsuwa.

- Zama mai bi fa zaka yi wanna baptisma a chikin ekklesiya Kristi. Matt 16:18, Galatiyawa 3:26-27.

- Zama mai bi ba bata lokachin  da yi baptisma Ayukan Manzanni 22:16;2Korinthiyawa 6:2 .

A KARSHE

Idan ka zama mai bi kamar yadda Littafin ta koyas sai zaka yi wadannan;

"Suka lizima a chikin koyasuwar manzanni da addu'oi.  Ayukan manzanni 2:42.

- Zaka chigaba a chikin bi Yesu Kristi Romawa 16:16.

- Zaka jinre a chikin bi Yesu Kristi, Ru'ya Ta Yohanna 2:10.

Tun da ka gane hanyar zama mai bi, sai ka ba da kan ka, a yi ma ka baptisma yau a chikin ekklesiya Kristi domin:

1.Ka tsira Markus 16:16,1Bitrus 3:21

2.Gafara zunubai ka- Ayukan Manzanni 2:38.

3 Wanke zunubai ka -Ayukan Manzanni 22:16

4. Ka shiga mulkin sama- Yohanna 3:3,5.

Sai ka yi tunani domin ka zama mai bi a yau a chikin sunan Yesu Kristi Amen.

 
| Home | Media | Languages | Free Stuff | Contact Us |

Powered by Joomla 1.5.20 | Template modified by WCBC.